Rundunar ’yan sandan jihar Nasarawa ta cafke wasu mutum biyu da ake zargin ’yan fashi da makami ne tare da kwato bindigogi a wani samame da ta gudanar a Lafia, babban birnin jihar. An bayyana cewa kamen ya biyo bayan bayanan sirri da jami’an tsaro suka samu.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Ramhan Nansel, ya ce an kama Kabiru Isah da Monday Bulus, wadanda ke cikin jerin mutanen da ’yan sanda ke nema, a ranar 10 ga Janairu 2026. Ya ce an cafke su ne yayin da suke shirin aikata fashi a cikin garin Lafia.

A cewarsa, an kwato bindigar G3 mara lambar rajista daga hannunsu, sannan wani samame na gaba a ranar 11 ga Janairu 2026 ya haifar da kwato bindigar pump-action. Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Shetima Jauro Mohammed, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin tare da umarnin a zurfafa bincike domin kamo duk masu hannu a lamarin.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version