Aƙalla mutum huɗu ne suka mutu a wani turmutsutsu da ya faru yayin rabon sadakar azumin Ramadan a unguwar Kofar-Guga da ke cikin birnin Katsina. Lamarin ya auku ne bayan taruwar jama’a masu yawa a gidan wani attajiri da ke raba sadaka a yankin.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, DSP Aliyu Abubakar, ya ce turmutsutsun ya faru da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar 26 ga Fabrairu, 2026. Ya ce jami’ai sun garzaya wurin bayan samun kiran gaggawa, inda aka kai waɗanda suka jikkata asibiti, sai dai huɗu daga cikinsu suka rasu daga bisani.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Bello Shehu, ya miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da ba da umarnin fara bincike. Rundunar ta shawarci masu niyyar raba sadaka su riƙa sanar da ’yan sanda tun da wuri domin a tanadi tsaro da tsari, don kauce wa sake aukuwar irin haka.


