Likitan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Dokta Bello Abubakar, na fuskantar bincike daga ƙungiyar da ke sa ido kan harkokin likitanci a Najeriya (MDCAN), bayan da Hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC) ta gurfanar da shi a kotu kan zargin bayar da rahoton jinya na bogi.

ICPC ta ce tana tuhumar likitan da laifuka huɗu, ciki har da bai wa jami’an gwamnati bayanan ƙarya da kuma amfani da rahoton jinya da ake zargin bai samu amincewar Asibitin Ƙasa da ke Abuja ba domin tallafa wa buƙatar belin El-Rufai. Haka kuma, an ce ƙwararrun likitoci daga Najeriya da Amurka sun tantance rahoton tare da bayyana cewa bai inganta ba.

Sai dai har yanzu kotu ba ta yanke hukunci kan zarge-zargen ba. Takardun kotu sun nuna cewa Babban Daraktan Kula da Lafiya na Asibitin Ƙasa zai bayar da shaida cewa rahoton bai samu amincewar asibitin ba, kuma ba a bi ƙa’idojin da suka dace wajen fitar da shi.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version