Mutane huɗu sun rasu, wasu da dama sun jikkata, yayin da daruruwan gidaje suka lalace sakamakon guguwar iska mai ƙarfi da ruwan sama da suka afkawa al’ummomin Ƙaramar Hukumar Kware a Jihar Sakkwato.

Lamarin ya kuma lalata gidaje da dama tare da yin ɓarna a muhimman cibiyoyin gwamnati, ciki har da makarantar firamare da asibiti. Hukumar NEMA ta kai ziyara domin tantance irin barnar da aka yi da kuma bukatun gaggawa na waɗanda abin ya shafa.

Rahoton farko na NEMA ya nuna cewa daruruwan iyalai sun rasa matsugunansu bayan gidajensu sun rushe ko suka lalace. Hukumar ta ce za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin jiha da na ƙananan hukumomi domin kai agajin jin ƙai ga waɗanda bala’in ya shafa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version