Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin sabbin shugabanni da mambobi 26 a hukumomi da kwamitocin gwamnatin tarayya guda 10. Sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar ta ce naɗe-naɗen sun fara aiki nan take.

Daga cikin waɗanda aka naɗa akwai tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, wanda zai jagoranci Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA), yayin da Manjo Janar Junaid Bindawa zai jagoranci Hukumar Albashin Ma’aikata ta Ƙasa.

Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Dr Abuh Mohammed a matsayin Darakta Janar na Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), Dr Akinola Odeyemi a matsayin shugaban NBET, Dr Anthony Inalegwu Godwin a Hukumar Makamashin Nukiliya ta Najeriya, Dr Abdullahi Maikano Saidu da Shuni Muhammad Dahiru na cikin sabbin mutane da shugaban ya naɗa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version