Rundunar ‘Yan sandan Jihar Jigawa ta kama mutane 10 da ake zargi da satar shanu, tumaki da kuma babur, wanda kimarsu ta kai sama da naira dubu 570,000 a yayin wani samame da aka gudanar don dakile ayyukan masu satar dabbobi a jihar. Mai magana da yawun rundunar, SP Shi’isu Adam, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, inda ya ce kama waɗannan mutane na daga cikin matakan da rundunar ke ɗauka wajen rage laifuka a yankin.

A cewar SP Adam, an kama wasu daga cikin masu laifin ne a ranar 22 ga Oktoba bayan samun kiran gaggawa daga al’umma game da satar dabba a yankin Balangu. Masu laifin sun haɗa da Muhd Jafaru, Gidare Kansila, Dare Kabo, Buba Umaru da Manu Musa, waɗanda ake zargi da haɗa kai wajen satar saniya ɗaya mai kimanin naira 450,000 da tumaki masu darajar naira 120,000. Rundunar ta ce an sami nasarar kwato dabbobin da aka sace kuma za a gurfanar da su a kotu nan ba da jimawa ba.

Haka zalika, a ranar 27 ga Oktoba, jami’an sashen Takur Site sun cafke wani matashi mai suna Mubarak Nasir, ɗan shekara 23, wanda ake zargi da satar babur a Dutse. Bincike ya nuna cewa Nasir ya amsa laifinsa, kuma shari’arsa tana kan tafiya. A wani samame daban a ranar 28 ga Oktoba, rundunar ta Hadejia ta kama wasu maza biyu, Ado Manu da Ibrahim Audu, daga ƙaramar hukumar Kiri Kasamma, bayan an same su da saniya da ake zargi da sacewa daga wani kauye da ake kira Zagari.

SP Shi’isu Adam ya tabbatar da cewa duk waɗanda aka kama za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike, tare da jaddada cewa rundunar ta ƙuduri aniyar kawar da satar dabbobi a fadin Jigawa. Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai don taimaka wa jami’an tsaro wajen yaki da masu aikata laifi.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version