Kwamishinan Ruwa na Kano Hon. Umar Haruna Doguwa ya mika takardar murabus daga mukaminsa a ranar Litinin, 2 ga Maris, 2026, kamar yadda Daraktan yaɗa labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanar, ya ce Gwamna Yusuf  ya karbi murabis din, tare da gode masa bisa sadaukarwa, biyayya, da jajircewarsa wajen hidimar al’umma da gwamnati, inda ya jaddada rawar da ya taka a matsayin Kwamishina na Ilimi kafin a sauya shi zuwa Ma’aikatar Ruwa.
A karkashin jagorancinsa, an samu ci gaba mai ma’ana wajen gyaran cibiyoyin ruwa da fadada isar da ruwan sha zuwa al’ummomi da dama a jihar. Gwamna ya bayyana cewa dogaro da kwarewarsa da ƙwazo ya taimaka wajen inganta ayyukan ma’aikatar da samar da ruwan sha mai ɗorewa ga jama’a.
Murabus din dai baya rasa nasaba da shirye shiryen da jamiyyar APC a Kano take yi na zaben sabon shugaba, inda majiyoyi ke cewa Doguwa ne ake sa ran zai zama sabon Shugaban jamiyyar ta APC a Kano

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version