Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta sanar da cafke mutane uku da ake zargi da hannu a kisan wata matar aure da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano. An kama su ne bayan wani bincike na sirri da aka gudanar daga daren 17 zuwa safiyar Lahadi 18 ga Janairu, 2026.
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Kiyawa, ya ce cafke mutanen ya biyo bayan umarnin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, tare da kulawar Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori. Ya bayyana cewa daya daga cikin ’yan uwan marigayiyar ya amsa laifin shirya harin da jagorantar kungiyar da ta aikata kisan.
A cewar ’yan sanda, an kwato kaya da dama daga hannun wadanda ake zargin ciki har da tufafi masu tabon jini, wayoyin marigayiya guda biyu, adda, sandar duka da kuma wasu kudade. Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin kamo sauran da ake zargi, tare da jinjina wa al’umma bisa hadin kai da kuma tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi a Kano.
