Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta tabbatar da kashe fiye da ’yan ta’adda 40 a wasu hare-haren sama da ta kai a yankunan Azir da Musarram da ke Jihar Borno. Hare-haren sun gudana ne a ranakun 15 da 16 ga Janairu, 2026, domin dakile shirye-shiryen kai hare-hare da kuma tallafa wa dakarun kasa.
Daraktan Hulda da Jama’a na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce an gudanar da farmakin ne bisa sahihin bayanan sirri da hadin gwiwa da dakarun Operation HADIN KAI. Ya bayyana cewa jiragen yakin NAF sun kai dauki cikin gaggawa a Azir, inda suka tarwatsa ’yan ta’addan da ke kokarin sake haduwa bayan ficewa daga fafatawa.
A cewarsa, an kuma kai wani harin katsewa a Musarram bayan gano ’yan ta’adda na taruwa a kan kwale-kwale domin kai hari a yankin Baga da Fish Dam. Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya jaddada kudirin NAF na ci gaba da kai hare-hare masu inganci don raunana karfin ’yan ta’adda da dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
