Wani kwararre a fannin lafiyar kwakwalwa, Dr. Olanrewaju Sodeinde daga Asibitin Neuropsychiatric na Aro, Abeokuta, ya bayyana cewa fiye da mutane miliyan hudu a yankin Kudu-Maso-Yammacin Najeriya na fama da shan miyagun kwayoyi. Ya ce alkaluman sun fito ne daga rahoton Hukumar UNODC, inda aka nuna cewa matsalar ta kai kashi 22.4 cikin dari a yankin.
Dr. Sodeinde ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wani gangamin wayar da kai mai taken “Kick Against Drug Abuse” da aka gudanar a Abeokuta. Ya ce akasin yadda ake zato, mata ma na cikin masu shan kwayoyi, inda ya nuna cewa daya cikin hudu daga masu shan miyagun kwayoyi mata ne, kuma adadin na karuwa a hankali.
A cewarsa, yawancin alkaluman na iya zama kasa da hakikanin gaskiya saboda tsoron kyama da kuma neman magani a wajen gargajiya. Ya kara da cewa sama da kashi 80 cikin dari na masu shigowa asibiti na da alaka da shan kwayoyi, lamarin da ke dora wa iyalai nauyin kudin jinya mai tsada, tare da kira ga gwamnati da iyaye su kara daukar matakan kariya da wuri.
