Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Jigawa ta cafke wani mutum mai shekaru 33, Lawan Isa, ɗan asalin Dorayi Karama a Kano, bayan an same shi da jabun dalar Amurka $100 guda 56. Kakakin rundunar, SP Shi’isu Adam, ya bayyana cewa an kama shi ne a ranar 5 ga Oktoba 2025 a Kasuwar Gidan Lage, ƙarƙashin Sashen ‘Yan Sanda na Ringim, sakamakon sahihin bayanan sirri da aka samu.
Bayan kama shi, jami’an tsaro sun gano wayoyin Android guda huɗu da kuma ƙaramar wayar a wajen wanda ake zargin. A cewar kakakin rundunar, Lawan Isa bai iya bayar da cikakkiyar hujja kan yadda ya samo kuɗin ba. An mika shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) a Dutse domin zurfafa bincike.
SP Adam ya jaddada cewa kama wanda ake zargin na cikin shirin ci gaba da yaki da aikata laifuka a fadin jihar. Ya bukaci jama’a da su ci gaba da kasancewa masu lura da tsaro tare da bayar da bayanai ga jami’an tsaro don tabbatar da zaman lafiya.
A baya-bayan nan, an gano cewa yawaitar jabun kuɗin dalar Amurka ta zama barazana a wasu jihohin Arewa, ciki har da Jigawa. A baya, rundunar ta kama wasu mutane 13 da ake zargi da hada-hadar jabun kuɗi da kuma damfarar jama’a ta hanyar yin kwangilar dala na bogi, tare da kwace kuɗaɗe da akwatunan bogi na Babban Bankin Najeriya. Hakan na kara nuna yadda wannan muguwar sana’a ke barazana ga tattalin arziki da tsaron al’umma.
