Wani ɗan Najeriya mai shekaru 37, Osinakachukwu Marcus Onu, ya rasa ransa bayan da ‘yan sandan zirga-zirga suka harbe shi a babbar hanyar N12 da ke Klerksdorp, a lardin North West na Afirka ta Kudu, da misalin ƙarfe 3 na safiyar Laraba, 17 ga Disamba, 2025. Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne yayin wani aikin binciken ababen hawa, inda ake zargin an bi motar marigayin kafin daga bisani a harbe shi.
Binciken ‘yan sanda ya tabbatar da cafke jami’an zirga-zirga huɗu masu shekaru tsakanin 25 zuwa 36 da ake zargi da hannu a kisan, bayan sun tsere daga wurin amma jami’an bincike suka gano su daga baya. An ce an same motar Onu a tsaye a tsakiyar hanya a ɗaya gefen N12, yayin da makaman jami’an da ake zargin an kwace su domin gwajin balistik, kuma ana tuhumarsu da laifin kisa da kuma ɓoye gaskiya.
Shugaban ‘yan sandan lardin na rikon ƙwarya, Manjo Janar Ryno Naidoo, ya yaba da saurin matakin da jami’an bincike suka ɗauka, yana mai cewa za a tabbatar an yi adalci. Wannan lamari ya ƙara tayar da hankalin ‘yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu, kasancewar ba shi ne karo na farko ba da ake samun rahoton kashe ‘yan Najeriya a ƙasar, lamarin da ke ƙara janyo kira ga kare haƙƙin baki da tsaro ga ‘yan ƙasashen waje.
