Akalla manoma 18 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wani hari da ‘yan bindiga suka kai kauyen Kawel da ke gundumar Mushere a Karamar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato. Shugaban matasan Bokkos, Christopher Luka, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin.

Luka ya bayyana cewa harin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na daren Lahadi, inda wani shugaban matasa ya sanar da shi cewa maharan sun bude wa mazauna kauyen wuta tare da kashe mutane fiye da 20, yayin da aka tabbatar da mutuwar mutum 18.

Ya ce nan take ya tuntubi jami’an tsaro da ke Bokkos, wadanda suka tabbatar masa da cewa sun samu rahoton harin kuma suna kan hanyarsu zuwa yankin. Ya bukaci hukumomin tsaro su dauki matakan gaggawa domin dakile rikicin kafin ya kara kamari, yayin da hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version