Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano tare da jami’an Nigeria Security and Civil Defence Corps sun fara bincike kan mutuwar wani jami’in sa-kai na Civil Defence a yayin wani shirin rabon tallafin Ramadan da Sallah a Ƙaramar Hukumar Tudun Wada.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne ranar Juma’a yayin wani shirin tallafi da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa, ya shirya. Kakakin ‘yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, ya ce jami’in ya rasa ransa ne bayan wasu bata-gari sun kai hari a wurin taron.
‘Yan sandan sun ce an garzaya da jami’in zuwa Asibitin Tudun Wada inda aka tabbatar da mutuwarsa kafin daga bisani a ajiye gawarsa a dakin ajiyar gawa na Aminu Kano Teaching Hospital. Hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike domin gano tare da cafke waɗanda suka aikata harin.


