Hukumar ’yan sanda a jihar Gombe ta tabbatar da cafke wasu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, tare da gano wasu motoci da aka sata da kuma bindigar gida. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa nasarorin da aka samu sun zo ne sakamakon sahihin bayanan leƙen asiri da tsauraran matakan sintiri da ake ɗauka a faɗin jihar.

A cewar rahoton, jami’an sintiri daga sashen Balanga sun dakile wata mota kirar Lexus Jeep da aka ɓoye asalin ta, bayan an sace ta a Abuja a ranar 5 ga Oktoba, 2025. An ce direban motar ya gudu bayan ya buge ɗan sanda da guduma, amma rundunar ta fara haɗin gwiwa da ’yan sandan Abuja domin cafke shi.

Haka kuma, rundunar ta cafke wani mutum mai suna Sani Bappari daga unguwar Mallam Inna bisa zargin satar mota kirar Honda Civic daga tsakiyar birnin Gombe. Jami’an leƙen asiri sun bi sawunsa, suka kama shi cikin dare, kuma suka kwato motar cikin ƙoshin lafiya.

Baya ga haka, wani mutum mai suna Augustine Nkwakoye daga Bolari Quarters ya shiga hannu bayan an same shi da bindigar gida da harsashi guda. Rahoton ya ce ya yi barazanar harbi a wajen garin tsohon Tipper Garage kafin a kama shi. Rundunar ta ce bincike yana ci gaba, tare da tabbatar da cewa Gombe za ta ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin mafi aminci jihohi a ƙasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version