Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta ƙara tsaurara matakan tsaro a faɗin jihar gabanin bukukuwan Sallah, bayan fashewar bom da ta auku a Maiduguri. Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya bayyana alhininsa ga gwamnati da al’ummar jihar Borno kan hare-haren da suka faru da yammacin ranar Litinin a wurare daban-daban.
Rundunar ta buƙaci al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu amma su kasance cikin shiri, musamman a wuraren taruwar jama’a. Wannan mataki ya biyo bayan taron Majalisar Tsaro ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati, inda jami’an tsaro suka tattauna halin da ake ciki tare da ɗaukar matakan kariya kafin Sallah.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Emmanuel Ado, ya umarci dukkan sassan rundunar su ƙara kaimi wajen tsaro a wuraren ibada, wuraren shakatawa da sauran muhimman wurare. Haka kuma rundunar ta gargaɗi matasa da direbobi kan ɗaukar makamai ko tuƙi cikin ganganci, tare da jaddada cewa za a hukunta duk wanda aka kama da abubuwa masu haɗari, yayin da ta bukaci jama’a su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai kan duk wani abu da ake zargi.


