Mai alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya umarci al’umma da su fara duban jinjirin watan Shawwal daga ranar Laraba, 29 ga watan Ramadan 1447, wanda ya yi daidai da 18 ga Maris, 2026. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata.
Sanarwar wadda Sambo Wali Junaidu ya bayyana, ta buƙaci duk wanda ya ga jinjirin watan da ya sanar da Hakimi ko Uban ƙasa mafi kusa da shi domin a kai rahoto ga Sarkin Musulmi. Haka kuma ya yi addu’ar Allah ya taimaka wajen cika wannan muhimmin aiki na addini.
Masarautar Sokoto Caliphate ta ce idan ba a ga watan a ranar Laraba ba, za a cika azumin Ramadan kwana 30, sannan a yi Sallah a ranar Juma’a. Amma idan an ga watan, za a gudanar da Sallar Idi a ranar Alhamis.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version