Rundunar ƴansandan Jihar Zamfara ta ce ta tare wata mota da ke ɗauke da abubuwan fashewa guda 954 da ake zargin za a kaiwa ’yan bindiga a jihar. Mai magana da yawun rundunar, Yazid Abubakar, ya bayyana cewa an kama direban motar mai suna Mustapha Mohammad.
Ya ce jami’an Task Force kan Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba ne suka gudanar da aikin a ranar 27 ga Janairu da misalin ƙarfe 4:15 na yamma, bayan samun sahihin bayanan sirri. An kama wanda ake zargin, mai shekara 38, yana tukin wata Toyota Corolla mai lambar KUJ 933 EJ, inda bincike ya kai ga gano abubuwan fashewar da aka ɓoye a cikin ledoji.
Ƴansanda sun ce binciken farko ya nuna ana shirin amfani da kayan ne wajen kera na’urorin fashewa na gargajiya. An mika kayayyakin da aka ƙwato ga sashen kula da abubuwan fashewa na rundunar, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano inda aka samo su, inda za a kai su da kuma sauran waɗanda ke da hannu a lamarin.
