Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin komawa jam’iyyar ADC a ranar Litinin, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar. Rahotanni sun nuna cewa zai bayyana hakan ne a Kano tare da tarbar shugabannin jam’iyyar ADC na ƙasa, ciki har da David Mark da Rauf Aregbesola.
An kuma ruwaito cewa Kwankwaso zai shiga ADC tare da tsohon mataimakin gwamnan Kano, Aminu Gwarzo, wanda ya ajiye mukaminsa a kwanan baya. Majiyoyi sun ce an shafe watanni ana tattaunawa da shi, inda ya nemi a ba shi kujerar mataimakin shugaban ƙasa kafin ya amince, amma daga baya ya amince da shiga jam’iyyar ba tare da sharadi ba.
Haka kuma, wasu jiga-jigan NNPP sun tabbatar da cewa Kwankwaso zai isa Kano domin shirye-shiryen sanarwar, inda ake sa ran taron zai jawo dimbin magoya baya. Sai dai jam’iyyar APC ta ce sauyin ba zai zama barazana ga sake zaɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ba, tana mai cewa Kwankwaso ba shi da isasshen ƙarfin siyasa a matakin ƙasa.


