Tsohon Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar Kebbi a zaben 2027. Malami ya tabbatar da hakan ne a wata hira da ya yi da DCL Hausa, inda ya ce yana da tabbacin samun goyon bayan jama’ar jihar gaba ɗaya.
Ya ce ko da yake ka’idojin INEC ba su ba su damar fara yaƙin neman zaɓe ba, lokacin da ya dace za a shaida irin goyon bayan da yake da shi. Malami ya jaddada cewa ya ɗauki shawarar tsayawa takara, kuma ba zai ja da baya ba, domin yana da rawar da zai taka wajen ceto jihar daga matsalolin da ta fuskanta.
Malami ya yi suka ga gwamnatin APC mai ci, yana zargin manufofinta da haifar da ƙarin talauci, musamman a Arewa. Ya ce tsaro ya tabarbare har manoma suka daina zuwa gona, sannan masana’antun shinkafa da suka dade suna aiki sun rufe saboda manufofi marasa amfani da gwamnati ta dauka.
Ya bayyana cewa kudurinsa shi ne ya inganta tsaro, farfaɗo da aikin noma, da kare muradun al’ummar Kebbi. Malami, wanda ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC a bana, yana cikin gungun ‘yan siyasar da ke neman kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a 2027.
