Gwamnatin Jihar Kano ta ce haɗin kan al’umma shi ne ginshiƙin dawo da martabar jihar, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar ƙalubale daban-daban. Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki, inda ya ce gwamnati za ta ba da cikakken goyon baya ga duk wani shiri na ci gaban Kano.

Ya tuna wa jama’a irin matsayin da Kano ta ke da shi shekaru da dama da suka wuce a fannonin ilimi, kasuwanci, noma da al’adu, yana mai cewa dawo da wannan martaba na buƙatar haɗin kai tsakanin kowane ɓangare na al’umma domin shawo kan matsaloli kamar shaye-shaye da rashin tsaro.

SSG ya bayyana cewa gwamnatin NNPP ta aiwatar da kashi 85 cikin 100 na alkawurran yaƙin neman zaɓe, tare da tabbacin cewa sauran za a kammala su nan gaba. Ya ƙara da cewa an fara shirye-shiryen sabbin tsare-tsaren ci gaba gabanin zaɓukan 2026 domin samar da Kano mai albarka da zaman lafiya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version