Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta gargadi Gwamnatin Tarayya kan abin da ta kira rashin adalci na son kai, tare da bayyana goyon bayanta ga tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami. A wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta ce dole ne a yi adalci cikin gaskiya da daidaito ba tare da la’akari da siyasa ba.

Jam’iyyar ta nuna damuwa kan yadda ake sauya wurin tsare wadannan jagororinta daga wata hukuma zuwa wata yayin da bincike ke gudana, tana mai cewa hakan na haifar da tambayoyi kan gaskiya da adalci. ADC ta bukaci a fito fili a bayyana matakin da bincike ya kai, tare da tabbatar da bin kundin tsarin mulki da kauce wa tsarewa ba bisa ka’ida ba.

Haka kuma reshen jam’iyyar na Kudu maso Kudu ya bukaci Department of State Services (DSS) ta zurfafa bincike kan harin da aka kai sakatariyarta a Edo da gidan jagoranta na kasa, John Odigie-Oyegun. Jam’iyyar ta ce kama mutum guda bai wadatar ba, tana neman a gano masu daukar nauyi da tallafin kayan aiki domin tabbatar da gaskiya da adalci.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version