Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi ta dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Abubakar Muhammad Kana Zuru, da kuma shugaban APC na Ƙaramar Hukumar Zuru, Aliyu Abubakar Abiola, bisa zarge-zargen rashin bin ƙa’idojin jam’iyyar.
Sakataren APC na jihar, Sa’idu Muhammad Kimba, ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne bayan koke-koken da masu ruwa da tsaki suka gabatar. Ya ce binciken da jam’iyyar ta gudanar ya tabbatar da zarge-zargen sakaci, rashin tuntuɓar masu ruwa da tsaki da kuma ƙin bin dokokin jam’iyyar.
Haka kuma, gwamnatin Jihar Kebbi ta dakatar da Kwamishinan Raya Kiwon Kifi, Alhaji Kabir Usman Alaramma, inda ta umarce shi da ya miƙa ayyukan ofishinsa da kadarorin gwamnati ga babban sakataren ma’aikatar. Sai dai gwamnati ba ta bayyana ko dakatarwar na da alaƙa da matakin da APC ta ɗauka ba.
