Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa Kwamitin Musamman Kan Yaƙi Da Shaye-Shayen Miyagun Ƙwayoyi da Safarar Su, a wani yunkuri na gwamnatin jihar na daƙile matsalar da ke ƙara addabar matasa da al’umma. An naɗa tsohon shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Kano, Barrista Muhuyi Magaji Rimingado, a matsayin shugaban kwamitin.

Kwamitin ya ƙunshi wakilai daga hukumomin tsaro, lafiya, addini da na gargajiya, inda aka ɗora masa alhakin tattara bayanan sirri, gano da rusa hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi, ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da kuma taimakawa wajen gaggauta gurfanar da masu laifi a gaban kotu.

Haka kuma, an ɗora wa kwamitin nauyin wayar da kan jama’a musamman matasa da ɗalibai game da illar shaye-shaye, tare da haɗa kai da malamai, sarakuna da ƙungiyoyin al’umma wajen yaƙi da wannan annoba. Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da amfani da dukkan hanyoyin da suka dace domin kare makomar matasan Kano da tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version