Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta gano motar ofishin gwamnan jihar, ƙirar Toyota Hilux, wadda aka sace kwanan nan daga fadar gwamnati. Wata sanarwa daga ofishin mataimakin gwamna ta tabbatar da cewa an gano motar ne da sanyin safiyar Laraba, sakamakon aikin haɗin gwiwa na gaggawa da jami’an tsaro suka gudanar.

A cewar sanarwar, an kuma kama wanda ake zargi da satar motar, wanda aka bayyana a matsayin cikakken ma’aikacin gwamnati da ke aiki a matsayin direba. Rahoton ya ce wanda ake zargin yana taimakawa ‘yansanda wajen gudanar da bincike domin gano cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru.

Ofishin mataimakin gwamna ya bayyana satar motar a matsayin babban cin amanar aiki, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta dauki matakin doka a kan wanda ake zargi don zama izina ga wasu ma’aikata.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version