Rundunar sojin Najeriya ta kama wasu jami’ai 20 bisa zargin shirya juyin mulki domin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Rahotanni daga majiyoyi sun bayyana cewa an kafa kwamitin bincike don gano gaskiyar lamarin, inda ake zargin sojojin da tsara kai hare-hare da kuma yi wa wasu manyan jami’an gwamnati kisan gilla, ciki har da Shugaba Tinubu, Mataimakinsa Kashim Shettima da shugabannin majalisun tarayya.

Majiyoyi sun ce wadanda ake zargi sun yi ta tuntubar juna tare da tsayar da ranar da za su aiwatar da juyin mulkin. Fallasa wannan shiri ya jefa gwamnati cikin fargaba, abin da ya sa aka soke faretin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai da aka shirya gudanarwa a ranar 1 ga Oktoba, saboda sojoji ne ke jan ragamar bikin.

Duk da haka, rundunar sojin ta musanta cewa akwai wani juyin mulki da ake shirin aiwatarwa. Kakakin rundunar, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya bayyana cewa rahotannin da ake yadawa ba gaskiya ba ne, yana mai cewa soke faretin na da nasaba da tafiyar shugaban kasa zuwa waje da kuma mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci.

Gusau ya ƙara da cewa binciken da ake yi kan wasu jami’ai 16 na al’ada ne, kuma yana da nufin tabbatar da ɗa’a da bin ƙa’ida a rundunar. Ya tabbatar cewa an kafa kwamitin musamman da zai bibiyi lamarin, kuma za a sanar da sakamakon binciken a lokacin da ya dace.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version