Jami’an tsaro a birnin Tripoli na ƙasar Libya sun kama wasu ‘yan Najeriya biyu a garin Qarabouli bisa zargin yaɗa saƙonnin da ke tunzura jama’a ta kafafen sada zumunta. Hukumomi sun ce mutanen sun rika wallafa bidiyo da wasu bayanai da ke ƙarfafa tashin hankali da ayyukan laifi.
Rahotanni sun nuna cewa hukumomin Libya sun ɗauki abubuwan da ake zargin sun yaɗa a matsayin karya dokokin ƙasar tare da barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma. Wannan ya sa aka gudanar da bincike kafin a ɗauki matakin kama su.
An bayyana cewa an kammala gurfanar da waɗanda ake zargin tare da miƙa su ga ofishin masu gabatar da ƙara domin ci gaba da bincike da yiwuwar shari’a. BechiHausa a ruwaito cewa hukumomin Libya na ƙara sa ido kan abubuwan da ake wallafawa a intanet domin dakile duk wani abu da ka iya barazana ga tsaron ƙasar.
