Gwamnatin Iran ta sanar da rufe babban birnin ƙasar, Tehran, a ranar Talata 7 ga watan Yuli, domin sauƙaƙa gudanar da jana’izar Ayatollah Ali Khamenei. Ta ce matakin zai kuma taimaka wa masu makoki fita daga birnin cikin sauƙi bayan kammala tarukan jana’izar.

Mai magana da yawun gwamnati, Fatemeh Mohajerani, ta ce an ɗauki matakin ne saboda yawan mutanen da ake sa ran za su halarci jana’izar. Haka kuma, gwamnatin ta ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar zaman makoki a faɗin Iran.

Ana sa ran za a binne Ayatollah Ali Khamenei a birnin Mashhad ranar Alhamis, yayin da aka tsara tarukan jana’iza daga 4 zuwa 8 ga watan Yuli a Tehran, Qom da Mashhad. Za a kuma gudanar da tarukan tunawa da shi a Bagadaza, Kazmin, Karbala da Najaf na ƙasar Iraq.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version