Jam’iyyar Allied People’s Movement (APM) ta bukaci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi cikakken bayani kan tiriliyoyin nairorin da aka ce an samu bayan cire tallafin man fetur tun daga watan Mayun 2023. Jam’iyyar ta ce ‘yan Najeriya na da hakkin sanin adadin kuɗin da aka tara da kuma yadda aka kashe su.
APM ta bayyana cewa duk da ikirarin gwamnati na cewa ana zuba kuɗaɗen cikin muhimman fannoni, har yanzu ba a fitar da cikakken bayani kan ayyukan da aka aiwatar da wuraren da aka gudanar da su ba. Ta ce hakan bai dace da ka’idojin gaskiya da riƙon amana ba.
Jam’iyyar ta kuma yi nuni da cewa tsadar rayuwa, hauhawar farashi da talauci sun ƙaru tun bayan cire tallafin mai. Saboda haka ta bukaci gwamnatin tarayya ta wallafa sahihin cikakken rahoto kan kuɗaɗen da aka samu, yadda aka kashe su da kuma irin sakamakon da suka haifar ga rayuwar ‘yan Najeriya.
