Kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki hudu domin fara biyan sabon tsarin albashin malamai da aka amince da shi. Shugaban kungiyar, Christopher Piwuna, ne ya bayyana hakan yayin wani taron lacca da aka gudanar a Jami’ar Sa’adu Zungur da ke Bauchi.
Piwuna ya ce idan gwamnati ta gaza fara aiwatar da sabon tsarin albashin cikin wa’adin da aka bayar, kungiyar za ta dauki mataki mai tsauri. Ya kara da cewa wannan bukata na daga cikin kokarin inganta walwalar malamai da kuma dakile matsalar karancin albashi da ke janyo kwararar kwararru zuwa kasashen waje.
Ya kuma bayyana cewa duk da yarjejeniyoyi da dama da aka cimma da gwamnati a baya, ana samun tangarda wajen aiwatar da su, lamarin da ke haifar da yawan sabani da yajin aiki.


