Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, tare da tsofaffin gwamnoni Aminu Tambuwal da Rotimi Amaechi, sun kai ziyara ga tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, domin jajanta masa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai. Rahotanni sun ce marigayiyar ta rasu ne a birnin Alkahira na ƙasar Masar bayan fama da jinya.
An ruwaito cewa an bai wa El-Rufai beli na ɗan lokaci daga hukumar ICPC domin ya samu damar halartar jana’izar mahaifiyarsa. A yayin ziyarar, Atiku ya bayyana cewa sun zo ne domin nuna goyon baya da ta’aziyya ga iyalan marigayiyar a wannan lokaci mai wahala, tare da yin addu’ar Allah ya jikanta.
Shi ma Tambuwal ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi da ba za a maye gurbinsa ba, yana mai cewa sun yi tarayya da iyalan wajen jimami. Ya kuma roƙi Allah da Ya gafarta mata kura-kuranta tare da ba ta Aljannatul Firdaus, ya kuma ba iyalanta haƙurin jure wannan rashi.


