Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya karyata rahotannin da ke cewa ya bai wa wani jami’in sojan ruwa, Laftanar Ahmed Yerima, sabuwar mota kirar Toyota SUV, bayan rikicinsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike.

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya fitar ta shafinsa na X a ranar Alhamis, Atiku ya bayyana labarin da ake yadawa a kafafen sada zumunta a matsayin ƙarya marar tushe. Ya ce bai taɓa ba wa Yerima ko wani mutum irin wannan kyauta ba, don haka ya bukaci jama’a su yi watsi da labarin.

Rahoton bogi da ya yadu a Facebook ya yi zargin cewa Atiku ya ba da kyautar motar ne domin nuna goyon baya ga jami’in sojan ruwan da wani sabani ya shiga tsakaninsa da Wike yayin da ministan ke duba wani fili da ake rikici a kai a unguwar Gaduwa, Abuja.

Bidiyon lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama, ciki har da tsohon Babban Hafsan Soja, Janar Tukur Buratai (rtd), suka yi kira da a nuna ladabi da mutunta dokoki da hukumomin gwamnati.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version