Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya bayyana goyon bayansa ga cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi, inda ya saba da ra’ayin Atiku Abubakar kan batun.

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya bayyana cewa zai dawo da tallafin idan aka zabe shi a 2027, yana mai cewa cire tallafin bai inganta rayuwar ’yan Najeriya ba. Sai dai Obi ya ce rashin amfani da kudaden da aka samu daga cire tallafin ba hujja ba ce ta mayar da shi.

Da yake magana a wani taro da kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta shirya a Fatakwal, Obi ya ce kamata ya yi gwamnati ta samar wa ’yan Najeriya wasu muhimman ayyuka da kudaden da aka samu daga cire tallafin. Ya zargi gwamnatin Tinubu da rashin amfani da kudaden yadda ya kamata, musamman wajen inganta kiwon lafiya.

Obi ya ce idan da an adana kudaden da aka samu daga cire tallafin, Najeriya za ta iya tara kusan dala biliyan 10 a asusun ajiyar dukiyar kasa. Ya kuma ce bai kamata a nemi ’yan Najeriya su yi sadaukarwa ba a lokacin da jami’an gwamnati ke ci gaba da yin almubazzaranci da kudaden jama’a.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version