Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci jam’iyyar APC da ta sake duba jerin sunayen mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓensa na 2027, bayan ce-ce-ku-ce da suka biyo bayan fitar da jerin sunayen. Wata majiya daga cikin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ta tabbatar da cewa an bayar da umarnin ne saboda wasu kura-kurai.

Majiyar ta ce daga cikin kura-kuran akwai sanya sunayen wasu jami’an gwamnati cikin kwamitin, yayin da wasu fitattun ’yan jam’iyyar da ake ganin ya kamata su kasance ciki ba su samu gurbi ba. Daga cikinsu akwai tsohon Gwamnan Filato Simon Lalong da Festus Keyamo, waɗanda suka taka muhimmiyar rawa a kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na 2027.

Sai dai jam’iyyar APC ta musanta rahotannin da ke cewa ta janye jerin sunayen mambobin Kwamitin Yaƙin Neman, kamar yadda Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Felix Morka ya bayyana a ranar Talata, ya ce jita-jita ce kawai, amma duk wani sauyi za a sanar da shi a hukumance.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version