Shugaban Donald Trump na Amurka, ya bayyana cewa hare-haren da Amurka za ta iya kai wa Najeriya zai iya kasancewa ta sama ko ta ƙasa, a matsayin matakin dakile abin da ya kira kisan gillar da ake yi wa Kiristoci a ƙasar.
A zantawar sa da manema labarai yace abubuwa da dama za su iya faruwa. Ya kara da cewa “suna kashe Kiristoci da yawa, ba za mu bari hakan ya ci gaba da faruwa ba.”
A ranar Asabar din da ta gabata ne Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa ya umarci Ma’aikatar Tsaro ta Amurka da ta fara nazarin yiwuwar kai hari ga Nigeria.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan ya bayyana cewa Kiristoci a Nigeria na fuskantar kisan kiyashi, kuma yana zargin masu tsaurin kishin Musulunci.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta mayar da martani tana cewa, Najeriya da Amurka ƙasashe ne masu alaƙa da ƙawancen yaki da ta’addanci, kuma tana sa ran ganawar shugabannin ƙasashen biyu za ta kawo fahimtar juna da mafita.
