Mabiya mazhabar Shi’a a Najeriya sun sake tunawa da cikar shekaru goma da kisan gillar da aka yi musu a Zaria, yayin da suka ce har yanzu suna cikin raɗaɗin abin da ya faru. A 2015 ne rikici ya barke tsakanin jami’an sojin Najeriya da mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky, lamarin da ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane da kuma jikkata da dama, bayan zargin Rundunar Soji cewa an tare musu hanya.
Farfesa Abdullahi Danladi, shugaban dandalin tattaunawa na IMN a Najeriya, ya bayyana wa BBC cewa a duk tsawon shekarun nan babu wani ɓangaren gwamnati da ya ɗauki mataki kan wadanda suka aikata kisan. Ya ce babu hukunci, babu kama, babu rahoton kwamitin binciken da aka kafa — abin da ya tabbatar musu cewa an yi ƙoƙarin rufe gaskiya. Ya ce hakan na ƙara tunzura zukatan mabiya Shi’a da kuma tabbatar musu da cewa an tauye musu adalci.
A cewar Farfesan, al’ummar Shi’a za su ci gaba da neman adalci muddin suna raye, tare da jaddada cewa tarihi ba zai manta da abin da ya faru a Zaria ba. Ya yi nuni da cewa ko da shari’a ta ɗauki lokaci mai tsawo, gaskiya dole ta bayyana wata rana. A cewar sa, wannan rana ta tunawa ta musamman ta sake tayar masu da raɗaɗin abin da ya faru, tare da ƙarfafa matsayarsu na kin yafiya.
Bechi Hausa ta tattaro cewa IMN na ci gaba da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su fitar da cikakken rahoto kan lamarin, tare da hukunta wadanda suka aikata kisan. Farfesan Danladi ya ce za su ci gaba da taruwa duk shekara, su fadakar da junansu game da wannan hari, domin tabbatar da cewa ba a manta da waɗanda suka mutu ba kuma an tabbatar da ganin adalci.
