Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya karyata wani labarin bogi da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke dangantashi da sukar shugaban Amurka, Donald Trump, game da zargin kisan mutane a Najeriya. Akpabio ya bayyana labarin a matsayin “kirkirar karya” da aka yi don tayar da rikicin diflomasiyya tsakanin Najeriya da Amurka.

Mai ba shi shawara kan yada labarai, Hon. Eseme Eyiboh, ya ce maganar da aka wallafa ta shafin Rant HQ ba gaskiya ba ce, kuma ba ta da wani tushe ko a rubuce ko da baki. Ya bayyana cewa hoton da aka haɗa da labarin — wanda ke nuna Akpabio tare da wasu sanatoci — an yi amfani da shi ne don yaudarar jama’a.

Eyiboh ya jaddada cewa Akpabio mutum ne mai daraja a duniya, kuma mai kishin zumunci da mutunta dangantaka tsakanin kasashe. Ya kara da cewa shugaban majalisar dattawan na daraja Trump a matsayin shugaba mai tarihi da kuma jagoran wata kasa mai girma. Ya kuma gargadi masu yada karya da su daina “rashin gaskiya ta kafafen intanet,” yana mai rokon jama’a da su yi watsi da labarin bogi.

Lamarin ya biyo bayan kalaman Trump a makon da ya gabata, inda ya ce Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana ta rayuwa, yana zargin ‘yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayi da kashe dubban mutane. Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce rahotannin da ke cewa ana zaluntar Kiristoci sun yi tsanani fiye da gaskiya, tana mai jaddada cewa gwamnati na ci gaba da kare rayuka da tabbatar da zaman lafiya tsakanin addinai.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version