Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya yi gargadi kan yadda gwamnoni masu ci, manyan jiga-jigan siyasa da shugabannin jam’iyyu ke taruwa a jihohin da ake gudanar da zaɓen gwamna da ba na ƙasa baki ɗaya ba. Ya ce hakan na iya yin barazana ga zaman lafiyar dimokuraɗiyyar Najeriya.

Jonathan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata, yayin da yake tsokaci kan zaɓen gwamnan Jihar Osun da aka gudanar a ƙarshen makon da ya gabata. Ya yaba wa INEC, hukumomin tsaro, jam’iyyun siyasa da al’ummar Osun kan yadda aka gudanar da zaɓen cikin lumana.

 

Sai dai tsohon shugaban ya nuna damuwa kan wata sabuwar dabi’a da ke kunno kai a harkokin siyasa, inda manyan jami’an gwamnati da shugabannin siyasa ke taruwa da dimbin magoya baya a jihohin da ake gudanar da zaɓen gwamna. Ya ce irin wannan yanayi na iya haifar da fargaba, tsoratarwa da matsin lamba ga masu zaɓe da abokan hamayya.

Jonathan ya ce bai kamata a bar siyasa ta koma fafatawar da ake ganin dole sai an samu nasara ko ta halin kaka ba. Ya yi kira ga ’yan siyasa da su ɗauki lamarin a matsayin batun ƙasa, domin tabbatar da cewa zaɓuka sun kasance cikin lumana da adalci, tare da ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version