Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ba zai janye daga takarar neman tikitin shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ba, yana mai zargin Shugaba Bola Tinubu da tsoma baki a harkokin cikin gida na jam’iyyun adawa.

Atiku ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar, inda ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi watsi da yunkurin jam’iyyar APC na tsoratarwa da raunana adawa kafin zaɓen 2027.

Maganganun sun biyo bayan rade-radin matsin lamba da ake cewa ana yi masa domin ya janye ya bar wa ɗan kudu damar tsayawa takara, musamman bayan shigowar Peter Obi ADC da kuma rahotannin yiwuwar haɗin gwiwa tsakaninsa da Rabiu Kwankwaso.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version