Hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a lokacin bikin Easter a arewacin Najeriya sun yi sanadin mutuwar akalla mutane 16 tare da raba da dama da muhallansu a jihohin Benue, Katsina, Kaduna da Borno. Lamarin ya haddasa firgici a yankuna daban-daban yayin da jama’a ke kokarin tserewa domin tsira da rayukansu.

A jihar Benue, wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai hari kauyukan Mbalom, Mbatsada da Agana inda suka kashe mutane 10 tare da jikkata wasu. A Kaduna kuwa, ‘yan ta’adda sun kai hari majami’u biyu a Ariko inda suka kashe mutane biyar tare da sace 31, amma daga bisani sojoji suka ceto su bayan fafatawa da maharan.

A Katsina, wani dan sanda ya rasu sakamakon hari a wasu kauyuka, yayin da a Borno ake zargin Boko Haram sun kai hari Awapul inda suka kona gidaje da shaguna ba tare da asarar rai ba. Hare-haren sun zo ne yayin da jami’an tsaro ke kara kaimi wajen dakile ayyukan ‘yan ta’adda a yankin.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version