Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta sake jaddada cewa samar da isasshen kudade ga jami’o’in gwamnati ne kadai mafita ta dindindin wajen kawo ƙarshen yajin aiki da kuma ɗaga matsayin jami’o’in Najeriya a duniya. Shugaban ASUU na ƙasa, Chris Piwuna, ya bayyana hakan ne a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Manyan Makarantu da TETFund a ranar Juma’a, inda ya ce matsalolin da suka jawo yajin aikin mako biyu na yanzu sun samo asali ne tun daga shekarar 2011. Ya bayyana cewa duk da amincewar Majalisar Dokoki da Naira biliyan 150 don jami’o’i, har yanzu an saki biliyan 50 kacal, kuma ma tana makale a Ma’aikatar Ilimi.

ASUU ta bukaci Majalisar Dattawa ta matsa wa gwamnati lamba domin ganin an fitar da dukkan kudaden da aka ware don jami’o’i, tare da amfani da su yadda ya kamata. Piwuna ya ce idan gwamnati ta ba da cikakken tallafi ga jami’o’i, za a kawo karshen yajin aiki da kuma inganta matsayin jami’o’in kasar a jerin na duniya. Ya kuma yi korafin cewa ministan Ilimi yana shirin raba kudaden da aka ware wa jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi, abin da ya sabawa tsarin rabon da aka amince da shi.

Haka kuma, kungiyar ta zargi Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, da yunkurin kwace wani bangare na filin da ya kai kadada 10,000 mallakar Jami’ar Abuja. ASUU ta bukaci Majalisar Dattawa ta shiga tsakani don kare filin jami’ar daga abin da ta kira yunkurin mamaye ƙasa da ba da izini ba. Ta ce duk wanda yake da niyyar bunkasa ilimi bai kamata ya zama barazana ga kadarorin jami’o’i ba.

A halin yanzu, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta biya yawancin bukatun ASUU, tana mai cewa tana bude ƙofa don tattaunawa. Sai dai ta aiwatar da manufar “ba aiki, ba albashi” kan mambobin kungiyar masu yajin aiki, yayin da rikicin ya ci gaba da yin tasiri kan harkokin ilimi a fadin kasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version