Hafsat Muhammad Sada daga Jihar Kano ta zama gwarzuwar shekara a ɓangaren mata a Gasar Karatun Alƙur’ani Mai Girma ta Ƙasa ta shekarar 2025, wadda aka kammala a ranar 20 ga Disamba, 2025, a Jihar Borno. Hafsat ta samu wannan babbar nasara ne bayan fafatawa da daruruwan ‘yan takara daga sassa daban-daban na ƙasar nan a gasar da ta kai karo na 40 a jerinta.

An sanar da sakamakon gasar ne daga bakin Daraktan Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci ta Jami’ar Usman Dan Fodio, Sakkwato, Farfesa Abubakar Yelwa, wanda ya bayyana cewa ‘yan takara 296 daga jihohi 30 ne suka shiga gasar a rukunoni shida. Nasarar Hafsat ta jawo hankalin mahalarta da jama’a, inda aka yaba mata bisa hazaka, nutsuwa da kwarewa a karatun Alƙur’ani.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa nasarar gasar da kuma yawan mahalarta, musamman mata, alama ce ta bunƙasar ilimin addini da dawowar zaman lafiya a jihar. Bechi Hausa ta rawaito cewa gwamnan ya jaddada muhimmancin bai wa mata dama a fagen ilimi, yana mai cewa irin wannan nasara na ƙarfafa gwiwar ‘ya’ya mata wajen rungumar karatun Alƙur’ani da ilimi gaba ɗaya.

Bikin kammala gasar ya samu halartar manyan baki ciki har da matar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Hajiya Nana Kashim Shettima, wadda ta jagoranci rabon kyaututtuka. Hafsat Muhammad Sada ta karɓi kyautar zakarun mata a cikin farin ciki da yabo daga mahalarta, lamarin da ya tabbatar da ita a matsayin gwarzuwar shekarar 2025 a ɓangaren mata a Gasar Karatun Alƙur’ani ta Ƙasa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version