Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    • Shafin Farko
    • Labarai

      Tinubu Ya Sha Alwashin Murƙushe Ta’addanci a Najeriya

      November 6, 2025

      Hukumar Kiyaye Afkuwar Haɗura Ta Ƙasa Ta Kama Direbobi 27,000 a Abuja

      November 6, 2025

      Gidaje 20 Da Ake Zargina a Kansu Ba Nawa Bane Ne Waɗanda Mahaifinmu Ya Bar Mana Gado Ne – Abba Kyari

      November 6, 2025

      Matuƙar Ba’a Yi Yadda Aka Yi a Afghanistan Ba Baza’a Kawo Ƙarshen Ta’addanci a Najeriya Ba – Amurka

      November 6, 2025

      Shekarau @ 70: Damuwa Bata Taɓa Hanani Bacci Ba – Shekarau

      November 6, 2025
    • Siyasa

      Gombe Na Amfana Da Cire Tallafin Man Fetur – Inuwa Yahya

      November 4, 2025

      Sabon Rikici Na Shirin Kunno Kai Tsakanin Sanata Natasha Da Akpabio

      November 4, 2025

      Har Yanzu Bamu Janye Dakatarwar Shekaru 30 Da Mu Ka Yi Wa El-Rufai Ba – SDP

      November 2, 2025

      Gwamnan Taraba Zai Koma Jam’iyyar APC

      October 29, 2025

      Gwamnonin PDP Sun Zaɓi Tanimu Turaki a Matsayin Ɗan Takararsu a Zaɓen Shugabancin Jam’iyya

      October 25, 2025
    • Addini

      Ƙungiyoyin Fityanul Islam Da Samarin Tijjaniyya Sun Yi Ƙarar Gwamnatin Kano a Kotu

      November 5, 2025

      Saudiyya Ta Ragewa Najeriya Kujerun Hajjin 2026

      October 17, 2025

      Sarkin Musulmi Ya Buƙaci a Samar Da Dokokin Amfani Da Kafafen Sada Zumunta a Najeriya

      October 16, 2025

      Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Laifin Yin Aure Ba Tare Da Amincewar Iyayensu Ba

      October 13, 2025

      Tinubu Ya Bawa NAHCON Umarnin Rage Kuɗin Hajjin 2026 Cikin Gaggawa

      October 7, 2025
    • Nishadi

      Oculus Founder Makes a VR Headset That Can Literally Kill You

      January 13, 2021
      85

      Braun Series 7 Electric Shaver Review: Quality at a Good Price

      January 13, 2021
      85

      Google Pixel 7, iPhone 14 Compared: Check Out 5 Major Differences

      January 13, 2021

      Why Apple Should Skip The MacBook Pro Launch

      January 12, 2021

      Apollo G2J Showcases Electric Sports Car

      January 12, 2021
    • Tsaro

      Sojojin Najeriya Sun Ƙwato lita 290,000 Na Man Fetur a Yankin Neja Delta

      October 21, 2025

      Ƴan Bindiga Sun Ƙwace Wayoyin Ƴan Sanda a Zamfara

      October 2, 2025

      Gwamnan Kano Ya Buƙaci Tinubu Ya Tsige Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar

      October 1, 2025

      Will Using a VPN on Phone Helps Protect You from Ransomware?

      January 14, 2021

      Popular New Xbox Game Pass Game Being Review Bombed With “0s”

      January 14, 2021
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    Home » CBN Ya Fitar Da Dala Biliyan 1.25 Don Shigo Da Man Fetur Duk Da Samuwar Matatar Dangote
    Featured

    CBN Ya Fitar Da Dala Biliyan 1.25 Don Shigo Da Man Fetur Duk Da Samuwar Matatar Dangote

    Abbass AbdurrahmanBy Abbass AbdurrahmanOctober 27, 2025No Comments2 Mins Read

    Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da dala biliyan 1.259 a watanni uku na farko na shekarar 2025 domin tallafa wa ‘yan kasuwar da ke shigo da man fetur da sauran kayayyakin mai, duk da cewa masana’antar Dangote ta fara samar da man cikin gida. Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin rage dogaro da shigo da mai daga ƙasashen waje.

    Rahoton Hukumar NMDPRA ya nuna cewa, duk da karuwar samar da mai daga masana’antar Dangote, ‘yan kasuwa sun shigo da kusan kashi 69 cikin 100 na man da aka ƙone a ƙasar tsakanin watan Agusta 2024 da farkon Oktoba 2025. CBN ta bayyana cewa dala miliyan 457.83 aka fitar a Janairu, sai ta sauka zuwa dala miliyan 283.54 a Fabrairu, sannan ta haura zuwa dala miliyan 517.55 a watan Maris – wanda ya fi sauran watanni yawan kuɗi.

    A cewar Kungiyar Dillalan Man Fetur ta IPMAN, dalilin da yasa ƴan kasuwa ke ci gaba da shigo da mai shi ne bambancin farashi. Kakakin ƙungiyar, Chinedu Ukadike, ya bayyana cewa ‘yan kasuwa na sayen mai daga inda suka fi samun riba, ko daga wajen Dangote ne ko kuma daga ƙasashen waje, domin farashin ne ke tantance kasuwa.

    Sai dai masana sun ce wannan shirin na CBN yana nuna sauyi a kasuwar man fetur, inda ake ganin matakan rage shigo da mai daga waje suna ƙara karɓuwa. Rahoton ƙarshe daga ƙungiyar MEMAN ya kuma nuna raguwar farashin shigo da lita ɗaya na man fetur zuwa N805.46, sakamakon sauyin farashin danyen mai da kuma canjin kudin waje.

    CBN
    Share. Facebook Twitter WhatsApp Telegram
    Previous ArticleFiye da Janar 500 Aka Tilastawa Barin Aiki Tun Daga lokacin Buhari zuwa Yanzu – Bincike
    Next Article Za a Yi Hazo Na Tsawon Kwanaki 3 a Wasu Sassan Najeriya – NiMet
    Abbass Abdurrahman
    • Website

    Related Posts

    Featured

    Tinubu Ya Sha Alwashin Murƙushe Ta’addanci a Najeriya

    November 6, 2025
    Featured

    Hukumar Kiyaye Afkuwar Haɗura Ta Ƙasa Ta Kama Direbobi 27,000 a Abuja

    November 6, 2025
    Featured

    Gidaje 20 Da Ake Zargina a Kansu Ba Nawa Bane Ne Waɗanda Mahaifinmu Ya Bar Mana Gado Ne – Abba Kyari

    November 6, 2025
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    SABBIN LABARAI

    Gwamnatin Kano Ta Dakatar da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi

    October 1, 202535 Views

    Kotu Ta Yankewa Tsohon Firayim Ministan Mali Hukuncin Zaman Gidan Yari Sakamakon Rubutu a Shafin Sada Zumunta

    October 27, 202533 Views

    Dantawaye Ya Zama Sabon Kwamishinan Ƴansanda a Abuja

    October 17, 202526 Views

    Zama a Banɗaki Fiye Da Kima Kan Haifar Da Matsala Ga Lafiyar Ɗan Adam – Likita

    October 28, 202520 Views

    Matuƙar Ba’a Yi Yadda Aka Yi a Afghanistan Ba Baza’a Kawo Ƙarshen Ta’addanci a Najeriya Ba – Amurka

    November 6, 202519 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    • Telegram
    © 2025 Bechi Hausa News. Developed by: ENGRMKS & CO.
    • Shafin Farko
    • Game da Mu
    • Ƙarin Bayani
    • Manufar Sirri
    • Ka’idoji da Sharudda
    • Tuntuɓe Mu

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.