Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sanar da naɗa Liam Rosenior a matsayin sabon babban kocin kungiyar. An tabbatar da nadin ne a ranar Talata 6 ga Janairu, 2026, kamar yadda kulob din ya bayyana a shafinsa na yanar gizo.

Rosenior, mai shekaru 41, ya taba taka leda a gasar Firimiya da Championship, kuma ya samu karɓuwa a fagen horaswa. Kafin ya komawarsa Chelsea, ya horas da RC Strasbourg inda ya kai kulob din samun tikitin buga gasar Turai karo na farko cikin shekaru 19, tare da rike mukamai a Hull City da Derby County a Ingila.

Chelsea ta ce Rosenior zai kawo sabbin dabaru da ƙwarewar jagoranci, tare da mai da hankali kan haɓaka ’yan wasa da gina ƙungiya mai tsari. Sabon kocin ya sanya hannu kan kwangilar da za ta kai har zuwa shekarar 2032, inda ya bayyana farin cikinsa da shirinsa na jagorantar kulob din zuwa nasarori a gida da Turai.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version