Yayin da damina ke kara karfi a Najeriya, cutar kwalara ta sake barkewa a wasu jihohin Arewa, inda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da kamuwa da dubban jama’a. Jihar Borno ce ta fi fuskantar matsalar, yayin da aka tabbatar da bullar cutar a Karamar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato.
Rahotanni sun nuna cewa Borno ta samu mutuwar mutum 74 da kuma mutane 7,850 da ake zargin sun kamu da cutar tsakanin farkon watan Mayu zuwa 9 ga Yuni. Haka kuma, sansanin ‘yan gudun hijira na Monguno ya samu mutane 296 da ake zargin sun kamu da kwalara cikin kwanaki uku kacal, mafi yawansu mata da kananan yara.
Masana kiwon lafiya sun danganta yaduwar cutar da rashin tsaftataccen ruwa, karancin muhalli mai tsafta da kuma cunkoson jama’a a sansanonin ‘yan gudun hijira. A halin yanzu, jihohin Benue, Taraba, Bauchi da Kebbi sun fara daukar matakan kariya da shiri domin hana barkewar cutar a yankunansu, yayin da hukumomi ke kira ga jama’a da su kiyaye tsafta da amfani da ruwa mai tsafta.

