Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da sabbin matakan tsaro domin daƙile ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane. Daga cikin matakan akwai haramta saye, sayarwa da jigilar fetur a cikin jarkoki a faɗin jihar baki ɗaya.
Sanarwar da Mai Bai Wa Gwamnan Shawara Kan Yaɗa Labarai, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar ta ce an ɗauki matakan ne bayan wani taron gaggawa na tsaro. Gwamnatin ta bayyana cewa bayanan sirri sun nuna ana amfani da fetur da ake kai wa cikin dazuka wajen tallafa wa ayyukan ‘yan ta’adda.
Haka kuma, gwamnatin ta rufe dukkan cibiyoyin POS da wuraren cajin waya na kasuwanci a ƙananan hukumomin Matazu da Musawa, tare da hana amfani da babura a yankunan. Gwamna Radda ya gargadi masu karya dokar da cewa za su fuskanci hukunci mai tsauri, yana mai jaddada aniyar gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

