Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya rasu yana da shekaru 100. Ɗansa, Sayyadi Ali Dahiru Usman Bauchi, ne ya tabbatar da mutuwar mahaifin nasa ga DailyTrust, inda ya ce, “Tabbas Sheikh ya koma wurin Mahaliccinsa. Dukkanmu daga Allah muka fito, kuma gare Shi za mu koma.”
Sayyadi Ali ya kara da cewa rayuwar Sheikh Dahiru ta cika da amfani kuma suna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya tsawaita rayuwarsa har zuwa wannan lokaci. Ya bayyana cewa har yanzu ba a yanke shawarar inda za a binne gawar Sheikh ba, ko a Abuja ko a Bauchi, domin shi a halin yanzu yana Madinah.
Sheikh Dahiru Bauchi ya shahara wajen bada gudunmawa a fannin ilimin addinin Musulunci da jagoranci a Najeriya, inda yayi tasiri a rayuwar dubban mabiya da dalibai.
Masoyan Sheikh da al’ummar Najeriya sun nuna alhinin rasuwarsa tare da addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, da kuma kara wa iyalansa hakuri a wannan lokaci mai girgiza.
