Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudiri na neman gwamnatin tarayya ta sake duba dokar mallakar bindiga domin bawa ɗaiɗaikun ‘yan kasa masu bin doka damar mallaka, sakamakon ƙarin tabarbarewar tsaro a jihohin Kwara, Kebbi da Neja. Dalilin kudirin ya biyo bayan hare-hare da garkuwa da mutane a makarantu, coci-coci da kauyuka, ciki har da harin da aka kai cocin CAC a Eruku ranar 18 ga Nuwamba, inda aka kashe mutane biyu aka yi garkuwa da 38 waɗanda daga bisani aka sako su. Sanatoci da dama sun jaddada buƙatar ɗaukar matakin gaggawa don dakile ta’addanci, fashi da makami, da yawaitar sace ɗalibai da ke tilasta rufe makarantu da dubban yara ke karatu.

A yayin muhawara, sanatoci sun yaba wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa soke tafiyarsa zuwa kasashen waje don jagorantar martanin tsaro wanda ya taimaka wajen kubutar da waɗanda aka yi garkuwa da su a Kwara da kuma ‘yan matan makaranta 24 na Kebbi. Sai dai wasu sanatocin sun bukaci bayyana wanda ya bayar da umarnin janye sojoji kafin sace ɗalibai a Maga, inda suka bayyana hakan a matsayin alamar matsalar cikin gida a hukumomin tsaro. Wasu kuma sun nuna damuwa kan kisan Brig-Gen Musa Uba da suka ce ya kara nuna tabarbarewar amincewa da dabarun tsaron kasa.

Shugaban marasa rinjaye da wasu sanatoci sun yi kira da a binciki yiwuwar masu fallasa tsari a cikin jami’an tsaro tare da tabbatar da sake fasalin tsarin tsaro cikin gaggawa domin karya karfin ‘yan ta’adda. Sanata Barau Jibrin ya jaddada cewa lamarin tsaro ba na gwamnatin tarayya kaɗai ba ne, inda ya bukaci gwamnatocin jihohi, kamfanoni, da al’umma su mara baya domin saurin shawo kan kalubalen tsaro. Ya kuma nemi jihohi su zuba jari a kayan sa-ido da hanyoyin tattara bayanan sirri domin taimakawa rundunonin tsaro su fi saurin daukar mataki.

Majalisar Dattawa ta kuma kada kuri’ar bukatar a yi gyara ga dokar bindiga domin ta dace da kalubalen tsaro na yanzu, kamar yadda kasashe sama da 175 ke ba da damar mallakar bindiga ga ‘yan kasa masu bin doka. Sanatoci sun ce lokaci yana kurewa, kuma dole ne gwamnati ta dauki tsattsauran mataki kan ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da miyagu da ke addabar al’umma. Sun ce rayuka na salwanta kuma wannan ba lokacin wasa ko nuna siyasa ba ne, domin matsalar na bukatar dabaru, kwarewa, da himma gaba ɗaya domin mayar da kasar kan turbar zaman lafiya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version