Jami’an Department of State Services (DSS) sun kama wata budurwa mai shekara 25, Nafisa Usman, dauke da harsasai 220 da aka boye a cikin garri a Kano. An cafke ta ne a wata tashar mota yayin da take karɓar kayan, bayan samun bayanan sirri daga jami’an tsaro.
Wadda ake zargin ta amsa laifinta inda ta ce tana karɓar harsasan ne daga wani jami’in soja da ke Lafia a Jihar Nasarawa, duk da cewa ba ta taɓa ganinsa ba. Ta kuma bayyana cewa tana karɓar kayan a Tashar Unguwa Uku, inda ake kai mata su a lokuta daban-daban.
Ta ƙara da cewa tana safarar harsasan ne zuwa ga ‘yan bindiga a dajin Kankara na Jihar Katsina ta hannun wani mai suna Mallam Haruna. A cewarta, ta kwashe kusan watanni biyu tana wannan harkar, inda ta yi mu’amala da ta kai kusan naira miliyan biyar kafin jami’an DSS su kama ta.
