Wasu ‘yan bindiga sun sace mutane tara tare da jikkata wasu biyu a ƙauyen Chacho da ke ƙaramar hukumar Wurno a Jihar Sokoto. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na dare ranar Laraba, inda maharan suka kutsa cikin ƙauyen ta wata hanya da ke haɗa yankin da dajin Sabon Birni.
Wani ɗan uwan ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa ya bayyana cewa maharan sun shigo ne yayin da mutane ke barci a waje, lamarin da ya sa jama’a suka rika tserewa domin ceton rayukansu. Ya ce sun ji karar harbe-harbe a wani ɓangare na ƙauyen, yayin da gidansu ke tsakiyar yankin.
Rahotanni sun nuna cewa an sace mata bakwai da tsofaffi maza biyu, yayin da wasu biyu suka jikkata kuma suna karɓar magani. Mazauna yankin sun koka kan ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga, inda suka danganta hakan da rashin isassun jami’an tsaro, yayin da ‘yan sanda suka tabbatar da harin amma suna ci gaba da tantance adadin waɗanda aka sace.


